Sports
Muna shiryawa dalibai wasanni domin hadakan daliban jami’ar —KUST Wudil.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jama,ar Aliko Dangote dake wudil tace tana shiryawa dalibai wasanni domin hadakan daliban jami’ar dan samun nassarori a makarantar.
mataimakin shugaban jami’ar farfesa musa Tukur Yakasai yace yaji dadi yadda yaga dalibain ke kokari wajen karatunsu kuma a bangaren wasaninni ma ba,a barsu a bayaba.
Mutum Miliyan 165 Sun Faɗa Ƙangin Talauci Cikin Shekara Uku – MMD
duk da zafin karatu irin na wannan makaranta da manyan fanni da makaranatar ke dashi.
Ya kara da cewa Zafin karatu na KUST wudil shine yasa muke shirya wa Dalibai wasanni.
Yakara da cewa zasu cigaba da bijiro da managartan tsare-tsare a fannin wasanin domin debewa daliban kewa yayin da karatu yayi tsanani,Sannan yayi kira ga daliban dasu cigaba da zage dantse domin su sami sakamako me kyau.
An kammala gasarcin kofi tsakanin fannonin dake makaranatar wanda ya gudana a jami’ar.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa duk shekara akan gudarda wannan wasa domin kara hadakan daliban jami’ar tare da nishadantar da daliban domin samun natsuwa wajan gudanar da karatu cikin jindadi da walwala, inda fannonin guda 6 dake jamia’r suka kara a wasan .
Wasan karshe ya gudana tsakanin fannin kimiya wato science dakuma fannin mona wato Agriculture,inda fangaran mona watoAgriculture, sukayi nassara daci 2 da 1 tsakanin su fannin kimiya wato science.
Kwamaret kamal Ado kibiya shine shugaban Daliban jami’ar yayi jan hankali akan wadan da sukazo na biyu a gasar da suzamo masu godiya ga Allah bisa samun kansu da sukayi a nabiyu .
Daga karshe kwamaret kibiya ya mika sakon bangajiya ga mataimakin shugaban makaranta da dukkan wadan da suka halarci kallon wasan dasu kansu yan wasan.
