Connect with us

News

Rasha ta kai hari tashar jiragen ruwan Ukraine

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Gwamnan yankin Odesa na Ukraine Oleh Kiper ya ce mutum guda ya mutu, sannan akalla mtum  15 sun jikkata, sakamakon harin da jiragen saman Rasha suka kai a tashar jirgin ruwa da ke yankin odesa na ukaine.

Advertisement

Ya ƙara da cewa harin ya kuma haifar da lalacewar ababen more rayuwa na fararen hula, da gine-ginen jama’a da kuma wata coci.

Gwamnatin jihar Filato ta musanta  cewa sama da shanu 1,000 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta

Birnin Odesa na fuskantar hare-hare a baya-bayan nan daga dakarun Rasha, tun bayan sanarwar da Moscow ta bayar a makon da ya gabata cewa ba za ta sabunta yarjejeniyar fitar da hatsi ba.

Advertisement

Tashar ruwa ta Odesa, ita ce tasha ra jiragen ruwa mafi girma a Ukraien, kuma an yi jigilar miliyoyin tan na hatsi daga tashar a ƙarƙashin yarjejeniyar da Turkiyya ta jagoranci ƙullawa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending