News
Gwamnatin jihar Filato ta musanta cewa sama da shanu 1,000 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta
DAGA KBIRU BASIRU FULATAN.
Gwamnatin jihar Filato ta musanta labarin da ake yadawa cewa sama da shanu 1,000 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta cikin kwanaki hudu a wasu kauyukan karamar hukumar Mangu ta jihar.
Daily trust ta ta ruwaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata cewa an yi ta yada labari a shafukan sada zumunta da kuma a wasu jaridun kasar kan yadda aka ce an kashe shanu.
Chelsea da Al-Hilal na gogayya kan Mbappe, Man Utd za ta sayi tagwaye
Sai dai gwamnatin jihar Filato a wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a ga gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ta ce labarin ba gaskiya bane.
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Filato kan wani labari da aka buga a wasu jaridun kasar nan kuma yana ta yawo a shafukan sada zumunta cewa sama da shanu 1,000 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta cikin kwanaki hudu a wasu kauyukan karamar hukumar Mangu ta jihar.
“Labarin da aka ce ya yi nisa da gaskiya, domin bai nuna gaskiyar abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummomin da aka ambata ba a cikin labarin. Domin kaucewa shakku, babu wani abu makamancin haka a yankin karamar hukumar Mangu kuma gwamnati ba ta samu labarin mutuwar dabbobi daga wata al’umma da aka ambata a cikin rahotannin ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
