News
Yan Sakandare Sun Yi Garkuwa Da Kansu, Sun Nemi Iyayensu Su Biya Kudin Fansa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Asirin wasu dalibai biyu ’yan sakandare ya tonu a lokacin da suka yi garkuwa da kansu tare da neman kudin fansa daga hannun iyayensu.
Rundunar tsaro ta Amotekun a Jihar Ondo ce ta kama daliban a wani otal da suka boye kansu a garin Oka-Akoko cikin Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma.
BARKEWAR CUTAR DIPHTHERIA: Kano Ce Ke Gaba Wajen Yawan Masu Fama Da Cutar.
Daya daga cikin daliban ta ce ta yanke shawarar yin garkuwa da kanta ne a dalilin tursasawar da mahaifiyarta take yi mata a kowane lokaci.
Ta ce ta hada baki da ’yar uwarta ne da suka kulla cewa za tayi amfani da kudin fansar ne wajen hukunta mahaifiyar da ta hana ta sakat.
Kwamanda Adetunji Adeleye ya ce daliban da aka kama da bai bayyana sunayensu ba masu shekaru 13 da 15, ’yan makarantar Sakandare (JSS 3) da (SSS1) ne da aka nuna su ga ‘yan jarida tare da wasu mutane 26 da ake zargi da aikata miyagun ayyuka a sassa daban daban na Jihar Ondo.
