Connect with us

News

Rundunar Yan Sanda Sun Haramtawa Masu Okada Sanya Takunkumin Hanci Da Hula.

Published

on

Dan sanda akan aiki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta haramtawa masu sana’ar tuka baburan Achaba, da aka fi sani da masu tuka okada, sanya abin rufe fuska da hanci wato Takunkumi da huluna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Inda ta gargadi mazauna garin da kada su hau baburan idan matukan suka sanya takunkumin ko hula.

Advertisement

Kotun ƙararrakin zaɓe a Kano ta amince da Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin halastaccen sanatan Kano ta tsakiya.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Mrs Yemisi Opalola, a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Osogbo, babban birnin jihar a ranar Litinin din nan ta sanar da dakatar da hakan.

Ta ce wasu masu babura sun sanya hula domin boye fuskokinsu ta hanyar rufe hancinsu da abin rufe fuska da hanci nufin aikata laifuka kamar fashi da fyade.

Advertisement

Ta ce, “Wannan gargadin ya zama wajibi saboda jerin rahotannin da rundunar ‘yan sanda ta samu cewa masu tuka babur suna amfani da hakan wajen aikata laifuka.

“An shawarci jama’a da kada su hau ko shiga abun hawan duk wani direban babur na kasuwanci tare da mai sanye da abin rufe fuska yayin aiki.”

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa PPRO ta yi kira ga shugabannin kungiyoyin masu tuka babura a jihar da su gargadi mambobinsu kan rufe kawunansu da fuskokinsu ta kowacce fuska yayin sana’arsu ta babur.

Opalola ta ce rundunar ta tsara dabarun kamawa da hukunta duk wanda ya karya dokar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending