Connect with us

News

Gobara ta lalata wasu sassan babbar kasuwar garin Yola.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Gobara ta lalata wasu sassan babbar kasuwar garin Yola.

Advertisement

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa da safiyar yau Talata cewa kasuwar ta tashi da wuta a daren Litinin yayin da yan kasuwar ke cikin gida.

Wane Hali Ake Ciki Kan Shirin Kungiyoyin Kwadago Na Fara Yajin Aiki A Najeriya ?

Wasu majiyoyi da dama sun ce shaguna da dama ne lamarin ya shafa, sannan gobarar ta yi sanadayar a sarar kayayyakin miliyoyin Naira.

Advertisement

Wani mazaunin da ke zaune a kusa da kasuwar ya ce, daukin gaggawa da jami’an kashe gobara suka yi ne ya ceci kasuwar daga barnar gaba daya.

Majiyar wadda ba ta fayyace musabbabin gobarar ba, ta ce kasuwar na da saurin barkewar gobara a duk shekara.

Advertisement

Hukumar kashe gobara ta jihar ba ta ce uffan ba kan lamarin, sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya ce an shawo kan lamarin.

Ya bayyana cewa nan take rundunar ‘yan sandan jihar ta samu rahoton barkewar gobarar, kwamishinan ‘yan sandan, CP Afolabi Babatola, ya tura karin jami,ai domin hana ’yan bata gari yin fashi a cikin kasuwar.
“Tare da goyon bayan ‘yan kwana-kwana, an shawo kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending