News
Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Advertisements
Advertisements
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Advertisements
Taron dai wani bangare ne na tuntubar shugaban kasar kan halin da ake ciki a Nijar.
Advertisements
Advertisements
Gwamnonin da suka gana da shugaban a Aso Rock sun hada da Ahmed Aliyu (Sokoto), Umar Namadi (Jigawa), Mai Mala Buni (Yobe), Idris Nasir (Kebbi) da Dr Dikko Radda (Katsina).
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS karkashin jagorancin Tinubu ta yi barazanar daukar matakin soji kan kasar Nijar, matakin da aka ki amincewa da shi a Najeriya.
Advertisements
