News
INEC Na Shirin Aikewa Da Na’urar BVAS Fiye Da Dubu 11 Domin Zaben Gwamna A Jahohin Bayelsa Da Imo Da Kuma Kogi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar zabe ta kasa INEC za ta tura na’urorin tantance masu kada kuri’a guda dubu 11 da 355 domin tantance masu kada kuri’a a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma Imo.
Wani babban jami’i a hukumar da aka sakaya sunansa ya bayyana haka ga wakilinmu a karshen mako.
Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.
A cewar INEC, jihar Bayelsa na da rumfunan zabe dubu 2 da 244 yayinda Kogi ke da rumfunan zabe dubu 3 da 508 sai Imo mai rumfunan zabe dubu 4 da 758.
Idan dai za a iya tunawa, zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, sun gamu da matsalar Na’urar BVAS.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
