Connect with us

News

Yan sanda sun tabbatar da sace basaraken gargajiya da matarsa a Nasarawa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace Sarkin Gurku, Jibrin Mohammed da matarsa ​​da wasu ‘yan bindiga suka yi a garin Gurku da ke karamar hukumar Karu a jihar.

DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya kara da cewa an yi garkuwa da sarkin ne a fadarsa.

INEC Na Shirin Aikewa Da Na’urar BVAS Fiye Da Dubu 11 Domin Zaben Gwamna A Jahohin Bayelsa Da Imo Da Kuma Kogi

A cewar Nansel, a ranar 6 ga watan Agusta, rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta samu kiran waya cewa wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka mamaye fadar garin Gurku mai tazarar kilomita 10 daga babban garin Mararaba a karamar hukumar Karu.

Ya kara da cewa bayan samun labarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, CP Maiyaki Mohammed-Baba, ya tura tawagar jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ’yan banga zuwa wurin.

“Da isowarsu, an gano cewa an yi garkuwa da basaraken da matarsa ​​zuwa inda ba a sani ba.

Advertisement

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa kwamishinan ya kara tura karin wasu mutane daga cikin tawagar kwararru da kuma masu yaki da masu garkuwa da mutane da kuma mutanen da suka fito daga yankin Karu zuwa wurin.

“Ana ci gaba da kokarin ceto basaraken da matarsa ​​ba tare da samun rauni ba. Za a sanar da jama’a yayin da al’amura ke faruwa,” inji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending