News
Sukar da Tinubu ke sha kan yunƙurin tura sojoji Jumhuriyar Nijar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na shan suka a gida game da barazanar da ya yi ta amfani da ƙarfin soja don kawo ƙarshen juyin mulkin da sojoji suka yi a maƙwabciyarsu Nijar.
‘Yan majalisar ƙasar sun tafka muhawara a kan batun ranar Asabar, inda suka ƙi goyon bayan matakin duk da cewa jam’iyyar APC ce mai mulki ke jagorancin majalisar.
Yawan Hadiman Da Gwamnan Jahar Kano Ya Nada Yanzu Sun Kai 81
Lamarin ya fi ƙamari musamman ga ‘yan majalisar da suka fito daga jihohin da ke da iyaka da Nijar mai tsawon kilomita 1,500, haka nan kuma ‘yan ƙasa da dama sun yi tir da yunƙurin.
Ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ce ta saka wa’adin ranar Lahadi da ta wuce ga sojojin da su sauka daga mulki ko kuma su fuskanci ƙarfin soja.
Ana kallon matakin a matsayin na Tinubu kaɗai saboda shi ne shugaban Ecowas, kuma Najeriya ce babbar mamba a cikinta.
Duk da cewa sojojin sun yi buris da wa’adin, Ecowas ba ta mayar da martani ba ta hanyar tura dakaru. Hakan ya kwantar da hankalin ‘yan Najeriya da dama, waɗanda suka fi son a bi hanyoyin difilomasiyya.
Da ma can wasu na ganin wa’adin kamar ba mai yiwuwa ba ne ganin cewa sai Najeriya da sauran ƙasashen Ecowas sun nemi amincewar majalisunsu kafin tura dakarun Nijar.
Kazalika, wasu sun yi mamakin yadda Najeriya ta katse wa Nijar wutar lantarki bisa umarnin Shugaba Tinubu, inda aka jefa babban birnin Yamai da wasu jihohi cikin duhu.
Masu sukar gwamnati na cewa hakan ya saɓa da yarjejeniyar da aka ƙulla wadda ta bai wa Najeriya damar gina madatsar ruwa a Kogin Neja, duk da cewa magoya bayan Tinubu kan ce an ɗauki matakin ne saboda a matsa wa sojoji su sauka daga mulki.
Najeriya da Nijar na da alaƙa mai ƙarfi ta fuskar tattalin arziki da al’adu, kuma duk wani yaƙi da za a kai wa Nijar zai shafi arewacin Najeriya, yankin da da ma tuni yake fama da matsalolin tsaro.
Wasu ƙungiyoyi na addini da fitattun ‘yan Najeriya da dama sun gargaɗi Tinubu game da “gaggawa wajen shiga rikici da maƙwabta saboda siyasar duniya”.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
