Connect with us

News

An Sauke Shugaban Wani Asibiti A Kano Saboda Zargin Yin Almundahana kudi.

Published

on

Likita

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta umarci shugaban Asibitin kula da masu larurar Mafitsara na Abubakar Imam Dr Atiku Adamu da kuma shugaban Likitoci na Asibitin Dr Kabiru Ahmad, dasu sauka daga kan matsayinsu a nan take, har zuwa lokacin da za’a kamma gudanar da bincike bisa zarginsu da aikata almundahanar kudi.

 

Advertisement

An dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen da aka samu wanda suka da karbar kudi daga hannun marassa lafiya, da tura marassa lafiya zuwa asibitoci masu zaman kansu domin yi masu magani ko kuma tiyata, da kuma zargin aikata lefin almubazzaranci.

Sukar da Tinubu ke sha kan yunƙurin tura sojoji Jumhuriyar Nijar

Wata sanarwa mai dauke dasa hannun jami’ar hulda da jama’a ta Hukumar, Samira Suleiman, Ta ce shugaban hukumar, Dr Mansur Mudi Nagoda ne ya bada umarnin, bayan amincewa da daukar matakin da kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya yi.

Advertisement

Arewa radio rawaito  cewar hukumar ta amince da yin sauyin wurin aiki ga daukacin ma’aikata da masu tarbar marassa lafiya zuwa wasu asibitocin, tare da maye gurbinsu da wasu batare da bata loakci ba.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending