Connect with us

News

Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta gargaɗi ECOWAS ta guji amfani da ƙarfin tuwo kan ƙasar Nijar

Published

on

Shugaban Kungiyar ECOWAS Bola Ahmad Tunibu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC ta gargadi kungiya haɓaka tattalin arzikin Afirka ta yamma wato ECOWAS da ta guji yin amfani da karfin tuwo wajen tunɓuke gwamnatin Sojin ƙasar.

NLC ta ce amfani sa ƙarfin tuwo wajen karɓar mulki a hannun sojin kasar lallai ba zai haifar da ɗa mai idanu ba.
Wannan gargaɗi yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi mai ɗauke da sa-hannun shugabanta Joe Ajaero.

Advertisement

Abubuwa 5 Da Ke Hana Waya Saurin Caji

Idan ba a manta ba dai a ranar Alhamis da ta gabata ne shugabannin ƙungiyar ECOWAS suka yibwani taron gaggawa inda suka ayyana cewa za su tura dakaru masu jiran ko-ta-kwana don maido da mulki zuwa hannun farar hula bayan da sojin ƙasar suka hamɓarar da shugaba Bazoum Mohammed.
Yayin taron na ECOWAS wanda shugaban Najeriya dake zama kuma shugaban ECOWAS din wato Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta, sun tsaida matsaya cewa amfani da karfin tuwo wajen ƙwace mulki a hannun sojin shine hanya mai ɓullewa.

Toh sai dai NLC ta ce matakin da ECOWAS din ke shirin ɗauka babu abinda zai haifar face jefa shugaba Bazoum da iyalansa dake tsare a hannun sojin cikin hatsari, kazalika makociyar Nijar ka-iya taka sawun ɓarawo.
Har-wa-yau ta ce muddin gwamnati ta san ba ta shirya ba toh kada ma ta fara domin ba a san menene zai kai ya komo ba.
“Babu shakka idan aka ce za a yi amfani da karfin tuwo, toh lallai akwai yiwuwar a maida Nijar wata matattara ta zubda jini”
“Kuma ko da bayan an gama yaƙin, toh tabbas akwai waɗanda za su ɓuya cikin rigar lamarin su ci gaba da tada ƙayar baya”
Bugu da ƙari NLC ta ce bisa ga dukkan alamu ECOWAS ta kasance ƴar amshin shata domin a cewarta babu makawa tana nuna ɓangaranci a lamuranta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending