News
Rikicin kabilanci ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu a Enugu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu ta ce an kama wasu mutane 12 da ake zargi da hannu a rikicin kabilanci da ya barke a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Ezeagu da ke jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Daniel Ndukwe, ya fitar a Enugu, ranar Lahadi.
Katsinawa na zanga-zangar goyon bayan Ecowas kan juyin mulkin Jahuriyar Nijar
Ndukwe ya ce rikicin tsakanin al’ummar Oyofo da Awha ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10 na safe.
“Kwamishanan ‘yan sanda, Mista Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin tura jami’an ‘yan sanda zuwa yankunan Oyofo da Awha.
Rikicin ya kai ga kashe maza hudu tare da kona babura uku da babura biyar,” in ji shi.
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon rikicin mallakar filaye tsakanin al’ummomin.
