News
Katsinawa na zanga-zangar goyon bayan Ecowas kan juyin mulkin Jahuriyar Nijar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Gomman masu zanga-zangar lumana sun fito kan titunan birnin Katsina don yin tir da da juyin mulkin sojoji suka yi a Jahuriyar Nijar tare da nuna goyon baya ga ƙungiyar Ecowas.
Rahotanni na nuni da cewa Masu macin ɗauke da kwalaye masu saƙonni iri-iri sun zagaya titunan birnin a safiyar yau Lahadi, a jihar da ke maƙwabtaka da Nijar.
A saki Bazoum,” kamar yadda ɗaya daga cikin kwalayen ke cewa. Wani kuma ya ce “muna tare da Ecowas”.
Ƙungiyar Coalition of Pro-Democracy Activists wadda ta shirya zanga-zangar, ta yi “kira da babbar murya ga sojojin mulki da su buɗe ƙofar tattaunawa da Ecowas don shawo kan matsalar”.