News
Rundunar ‘Yan sanda jahar katsina sun kashe ‘yan ta’adda, tare kwato tumaki 60
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya tare da harsashi 110 na 7.62MM.
Sun kuma kwato tumaki 60 da barayin suka yi awon gaba da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun mamaye kauyen Korogo ne a ranar 15 ga watan Agusta, 2023, ta hanyar Daddara, karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda suka yi ta harbe-harbe ba tare da bata lokaci ba.
Majalissar Malamai Bada Umarnin Dakatar Da Shirin Bukukuwan Addinin Gargajiya A Jihar Kwara
Da samun rahoton DPO Jibia ya tara tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wajen da lamarin ya faru inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan cikin wani mugunyar bindigu, lamarin da ya tilasta musu yin watsi da wannan mugunyar aikin nasu, inda suka bace cikin daji.
Sai dai ASP Sadiq ya ce an kashe daya daga cikin wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne, haka kuma an kwatu tumaki sittin (60), da kuma bindiga kirar AK-47 guda daya da alburusai dari da goma (110) mai girman 7.62mm. harsashi, an kwato. Ana ci gaba da bincike.”