News
Jam’iyyar NNNP Ta Ce Ba Ta Dakatar Da Kwankwaso Ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya karyata zargin dakatar da Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023.
Babban mai binciken jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Laraba a hedikwatar NNPP na kasa da ke Abuja.
GWAMNATIN KANO TA TSARA HANYOYIN WARWARE MATSALOLIN BASHIN DA MASU SAYAR DA MAGUNGUNA KE BIN DMCSA
Johnson wanda tsohon mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Kwankwaso ne ya bayyana cewa dakatarwar ba gaskiya bane ba.
Wani bangare na jam’iyyar karkashin jagorancin tsohon shugaban kwamitin amintattu (Boniface Aniebonan) ya dakatar da Kwankwaso a ranar Talatar da ta gabata na tsawon watanni shida bisa zarginsa da cin hanci da rashawa bayan wani taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) daya gudana a Legas.
Haka kuma ta nada tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Manjo Agbo a matsayin shugaban riko na kasa.
Johnson, ya ce an dakatar da Aniebonam da Agbo na tsawon watanni uku a ranar 24 ga watan Agusta saboda aikata wasu abubuwa marasa kyau kafin daga bisani a kore su daga jam’iyyar.
Ya kara da cewa, a taron da hukumar zabe ta jam’iyyar ta gudanar a ranar Talata a Abuja, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanyawa ido, ta dauki wasu matakai da suka hada da zaben sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa, sauya tambarin jam’iyyar, da korar Aniebonam da kuma korar shugaban jam’iyyar.
“Shin ba abin dariya ba ne ace duk mutanen da aka dakatar ko aka kore su sun taru a wani wuri su ce sun dakatar da Kwankwaso su kuma rushe NWC?
“Masu barkwanci sun kuma nada CTC wanda ya kunshi mutanen da suka daina zama mambobin jam’iyyar ta hanyar tsarin mulkin mu,” in ji