News
Kasheem Shettima ya buƙaci NAHCON da ta sake duba tsarin ciyar da Alhazai a ƙasa mai tsarki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shetima ya buƙaci hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON da ta yi kira ga mahukuntan kasar Saudiyya da su janye matakin da suka dauka na samar da abinci ga alhazan Najeriya a cikin kwanaki 5 na aikin Hajjin a kasar Saudiyya.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Shugabannin gudanarwar Hukumar domin bayyana masa sakamakon aikin hajjin shekarar 2023 a yau a fadar shugaban kasa da ke Villa a Abuja.
GWAMNATIN KANO TA TSARA HANYOYIN WARWARE MATSALOLIN BASHIN DA MASU SAYAR DA MAGUNGUNA KE BIN DMCSA
Ya ce duba da sauyin yanayi da ake fama da shi a duniya ya zama wajibi ƙasar ta Saudiyya da ta baiwa hukumar jin dadin Alhazai ta Jiha damar ciyar da Alhazanta domin kaucewa rashin jin dadi na jiki ko na lafiya a lokacin aikin Hajji.
Ya ƙara da cewar, yana da mahimmanci Saudiyya ta sake duba tsarin jin daɗin alhazan tare da duba sauyin yanayi, yana mai cewa da yawa daga cikin Mahajjata idan ba a ciyar da su da kayan abinci na gida ba za su iya samun ƙarfin jiki wajen gudanar da aikin Hajjin ba wanka kuma shine babban dalilin zuwa ƙasa mai tsarkin.
Don haka ya buƙaci hukumar da su jawo hankalin Saudiyya wajen yin la’akarin tattalin arziki domin kyautata jin dadin Alhazai.
Sanata Shettima wanda ofishinsa ke sa ido a yanzu haka ya yabawa hukumar gudanarwar bisa nasarar kammala aikin Hajjin 2023 tare da bukatarsu da su tashi tsaye wajen fadakar da jama’a kan aikin Hajji na 2024 domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin bana cikin sauki.
Tun da farko a jawabinsa Shugaban Hukumar NAHCON Alhaji Zikiruah Kunle Hassan ya yi wa mataimakin shugaban kasa karin haske game da aikin Hajjin 2023 da hanyoyin da ake bi wajen shirye-shiryen Hajjin 2024.
A cewarsa aikin Hajjin 2023 bai rasa nasaba da ƙalubale ba amma tare da goyon baya da kuma sa hannun mataimakin Shugaban ƙasa Musamman Wajen bayar da kuɗaɗe ga hukumar an shawo kan matsalolin.
Shugaban wanda ya bayyana wasu nasarorin da hukumar ta samu tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2020, ya ce tsarin tanadin aikin Hajji (HSS) Cibiyar Alhazai ta Najeriya (HIN) da bunkasar tattalin arziki na daga cikin shirye-shiryen kawo sauyi don tabbatar da dorewar tattalin arzikin Alhazai.
Tawagar Shugaban ta haɗa da Kwamishinan tsare-tsare na hukumar, Ma’aikata da Shugaba mai kula da sashen Kudi (PPMF) Alhaji Nura Hassan Yakassai Kwamishinan Ayyuka da Lasisin Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa Kwamishinan Tsare Tsare-Tsare na Ƙididdiga da Lantarki (PRSILS) Sheikh Suleman Momoh, da Sakatare
na Hukumar Dr Rabiu Kontagora da kuma tarin ma’aikatan gudanarwa na Hukumar.