News
Mata masu ciki idan suna shan Sigari akwai yiwuwar Jaririn da yake cikinsu ya kamu da cutar Asma
DAGA FATIMA SULAIMAN SHU’AIBU
Hukumar lafiya ta duniya WHo ta bayyana yadda mutum million daya da dubu dari tara kan mutu wa duk shekara saboda shan taba sigari da kuma shisha
Jaridar Indaranka ta rawaito cewa Taba dai nau’ine na ganye wadda ake nomawa a kuma siyarwa da manyan kamfanoni domin su sarrafata.
Wasu na Shan taba cigari ne domin nishadi, yayin da wasu kuma na shan tane domin burgewa a yayin kuriciya Wasu kuma domin burgewa da sauran mabanbantan ra’ayoyi.
Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da tallafin karatu ga daliban da suka kammala karatun digiri
To saidai kuma masana kiwon lafiya sun bayyana illolin da shan tabar ka iya haifarwa ga lafiyar masu ta’ammali da ita
Bincike ya tabbatar da cewa Shan taba Sigari yana sanadiyyar mutuwar Matasa sama da mutum 480,000 (dubu dari hudu da tamanin) duk shekara
Akasar Amurka kadai. Sama da mutane MILIYAN SHA-SHIDA(16,000,000) ne suke fama da cututtuka daban daban wadanda suke da alaka da shan taba Sigari.
Anyi kiyasin cewa sama da mutane miliyon 88 ne suke cutuwa ta dalilin Sigarin da Waninsu yake sha. Kuma Mutane Miliyon 41 ne suka rasu ta dalilin shaqar hayakin da masu shan taba suke hura musu.
Sigari ita ce sanadiyyar kashi 90 (90%) na cututtukan Sankarar hunhu mai saurin Kisa (Lung Cancer).
Kuma ita ce sanadiyyar kashi ‘daya cikin uku (33%) na duk wata cutar Daji (Cancer) wacce take damun ‘yan Adam.
Kazalika binciken ya kara tabbatar da cewa Mata masu ciki idan suna shan Sigari akwai yiwuwar Jaririn da yake cikinsu ya kamu da cutar nan ta Asthma. Ko kuma suyi bari, ko kuma su haifi yaron acikin wani irin yanayi.
Sigari tana shiga hanyoyin jini, tana gurbatashi, tana toshe ƙofofi da zuciyar Dan adam.
