News
Kotun Kasar Faransa ta amince a haramta wa dalibai sanya abaya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babbar kotun Kasar Faransa ta amince da matakin gwamnatin kasar na haramta wa dalibai sanya abaya a makarantun kasar.
Kotun ta yi watsi da karar da wata kungiyar Musulmai ta shigar tana kalubalantar matakin, wanda gwamnatin Emmanuel Macron ta dauka a watan jiya.
Gwamnan Ondo Ya Dawo bayan shafe kimanin wata uku yana jinya a kasar Jamu
A wani Labarin kuma Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.
Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.
Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.
Gwamnan Ondo Ya Dawo bayan shafe kimanin wata uku yana jinya a kasar Jamu
Kotun ta ce haramta sanya abaya ba nuna wariya ba ne ga Musulmai.
“Wannan haramcin bai keta hakkin gudanar da addini da neman ilimi … ko kuma tsarin nuna wariya ba,” in ji sanarar da kotun ta fitar.
Ranar 31 ga watan Agusta, Vincent Brengarth, lauyan kungiyar Musulmai ta Muslim Rights Action (ADM), ya shigar da kara a gaban kotun inda ya bukaci ta dakatar da gwamnati daga haramta sanya abaya, matakin da ya ce ya keta ‘yanci daban-daban na dan adam.
Ministan Ilimin Faransa Gabriel Attal ya ce dalibai kusan 300 ne suka bijire wa dokar haramta sanya abaya ranar Litinin lokacin da aka sake bude makarantu bayan an yi hutu.
Yawancinsu sun amince su sauya tufafin da ke jikinsu amma 67 sun ki yarda su cire abaya, kuma an kore su gida, a cewar ministan.
A watan jiya ne gwamnati ta sanar da haramta sanya abaya a makarantu, tana mai cewa Faransa kasa ce da ke raba harkokin kasa da na addini.
Matakin ya faranta ran masu tsattsauran ra’ayi amma masu sasaucin ra’ayi sun ce hakan take hakkin mata Musulmai ne.