News
Babbar Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Sake Lalacewa
![](https://indaranka.com/wp-content/uploads/2023/09/FB_IMG_1695142166544.jpg)
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Bayan mako guda da ‘Yan Nijeriya suka kasance cikin duhu, Tashar samar da wutar lantarki ta kasa ta sake lalacewa.
An bayar da rahoton cewa wutar lantarki ta ragu daga megawatts 3,594.60 (MW) zuwa 42.7MW da misalin karfe 1 na daren ranar Talata.
Atiku Ya Daukaka Kara Kotun Koli Yana Neman A Soke Hukuncin Da Kotun Sauraren Karar Zabe Ta Yanke
A cewar Guardian, tashar wutar lantarki ta Delta ce kawai ke aiki akan babbar tashar da 41.00MW a wuraren karfe 12 na rana yayin da Afam ke da 1.7MW.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyar kacal bayan babbar tashar ta lalace sau biyu cikin sama da sa’o’i 12 da barin ‘yan Nijeriya daga cikin duhu.
Idan dai za a iya tunawa, an dawo da wutar lantarki a Nijeriya ‘yan sa’o’i bayan da aka daina jin duriyar wutar da aka yi a fadin kasar a ranar Alhamis din da ta gabata, sakamakon lalacewar na’urar samar da wutar lantarki ta kasa (TCN) daga Osogbo a jihar Osun.
Kwanaki kafin faruwar lamarin, Ministan wutar lantarki na Nijeriya, Adebayo Adelabu ya yi ikirarin cewa fashewar wani abu a Kainji/Jebba 330kV ne ya janyo lalacewar wutar lantarkin ta kasa da sanyin safiyar ranar Alhamis din da ta gabata.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin jerin sakonnin twitter da ya aike a dandalin X yayin da yake tabbatar da cewa dukkansu suna kan aiki don tabbatar da dawo da wutar lantarki cikin gaggawa.
Wani labarin kuma Atiku Ya Daukaka Kara Kotun Koli Yana Neman A Soke Hukuncin Da Kotun Sauraren Karar Zabe Ta Yanke
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro