News
Cutar Mashako Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 14 A Jihar Jigawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da bullar cutar sarkewar numfashi wato (cutar mashako) a jihar.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar, Dr. Salisu Mu’azu Babura, ne ya tabbatar da hakan.
Muazu ya tabbatar da cewa kimanin mutane 91 da ake zargin sun kamu da cutar.
Rundunar ’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Bindiga Ɗauke Da Makamin Roka A Jahar Yobe
Kazalika ma’aikatar lafiya ta jihar tace a kwai rahoton yara goma da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar.
Dakta Salisu Mu’azu, ya ce sun gano wasu mutane biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun. Salisu ya ce yanzu haka an tura karin samfurin jinin wadanda ake zargin sun kamu da cutar zuwa Abuja domin yin gwaji.
Wani labarin kuma Rundunar ’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Bindiga Ɗauke Da Makamin Roka A Jahar Yobe
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro