Entertainment
Naira Marley Yace Bashi Da Hannu A kashe Mohbad kuma Ni Ba Dan Kwaya ko Kungiyar Asiri
Muhammad Muhammad Zahraddin
Mawaƙin kasar nan , Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley ya sake jaddada iƙirarinsa na cewa ba shi da hannu a kisan tsohon abokin aikinsa, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.
Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da daddare, Naira Marley ya ce, kamar kowa, shi ma ya shiga cikin damuwa sosai sanadiyyar mutuwar tsohon yaron aikin nasa.
Naira Marley ya ce Mohbad ya bar kamfanin ‘Marlian Music’ ne a watan Satumban 2022, sai dai ya ƙara da cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu ba ta kai yadda ɗaya daga cikin su zai riƙa yi wa ɗan’uwansa fatan mutuwa ba.
“Gaskiya ne cewa mun samu saɓanin fahimta a lokacin da muke aiki tare, amma saɓanin bai kai yadda mutane ke zuzutawa ba. Bai kai yadda za mu yi wa juna fatan mutuwa ba.” In ji Naira Marley.
Ya kuma ce sun riƙa ƙoƙarin warware rashin jituwar ta hanyar shari’a gabanin mutuwar Mohbad.
Marley ya ce dalilin da ya sa ya yi gum da bakinsa game da mutuwar ta Mohbad shi ne saboda kaɗuwar da ya yi, da kuma gudun kada ya kawo cikas ga binciken da jami’an tsaro ke yi kan mutuwar.
Ya kuma ƙara da cewa ya bar Najeriya ne tun a ranar 31 ga watan Agusta, kuma bai dawo ba tun wancan lokacin, sai dai yanzu haka yana shirye-shiryen dawowa domin amsa gayyatar ƴan sanda
Naira Marley ya kuma ce kamfaninsa ba cibiyar ta’ammuli da ƙwayoyi ko ƙungiyar asiri ba ne. Inda ya ce shi kansa ba mai safarar ƙwaya ko ɗan ƙungiyar asiri ba ne.
Ya ce “Marlian Music kamfani ne na wasu aminan juna, waɗanda ke gudanar da ayyukansu ta halastacciyar hanya. Manufarmu ita ce yin jagora ga mutane masu basira da tallafa musu.”
A ranar 12 ga watan Satumba ne Mohbad, mai shekaru 27 a duniya ya rasu, inda yanzu haka jami’an hukumar tsaro ta DSS ke gudanar da bincike kan mutuwar tasa.
Lamarin ya kai ga cewa an sake tono gawar mamacin bayan binne ta domin gudanar da bincike, inda yanzu haka ake jiran sakamako.
Mutuwar Mohbad ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya da ƙasashe maƙwafta, musamman a shafukan sada zumunta.