News
Lauyoyin Atiku Sun Shigar Da Kara Suna Kalubalantar Zuwan Tinubu Jami’ar Chikago

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tawagar lauyoyin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar sun shigar kara suna kalubalantar bulaguron shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zuwa jami’ar jihar Chikago domin hana sakin takardun karatunsa.
Mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa Prank Shuaibu ya bayyana haka ga jaridar Punch, cewa tawagar lauyoyin zasu martani bayan kusan sa’o’I 48 kan karar a kotun Amurka.
Gwamnan Kano Zai Kashe Naira Miliyan 600 Wajen Gudanar Da Ayyuka A Kasuwar Hatsi Ta Dawanau
Tun da farko dai Atiku ya samu sahalewar kotun domin samun bayanan karatun shugaban kasar ga lauyoyinsa.
Maisharia Jeffrey Gillbert a makon daya gabata ya bayar da umarnin sakin bayanan karatun cikin kwanaki.
Atiku dai na kalubalantar nasarar tsohon gwamnan jihar a zaben 2023, da kuma hakucin kotun saurarar kararrakin zaben shugaban kasa.
Bayanan da dan takarar jam’iyyar PDP ya samu, ta hannun lauyoyinsa, sun hada da tarihin shigar sa jami’ar, da kuma bayanan ranar da ya fara karatu, bayanan yau da kullum, da kyaututtuka da Bola Tinubu ya lashe da sauran abubuwa. Sai dai a yau alhamis ne wa’adin da mai shari’a Gilbert ke karewa, lauyoyin shugaban kasa Tinubu sun garzaya Maldonado inda suke rokon soke hakuncin mai shari’a Gilbert da ya bayar da damar dubawa da kuma bincikar tarihin.
Wani labarin kuma Gwamnan Kano Zai Kashe Naira Miliyan 600 Wajen Gudanar Da Ayyuka A Kasuwar Hatsi Ta Dawanau
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro