News
Gwamnan Kano Zai Kashe Naira Miliyan 600 Wajen Gudanar Da Ayyuka A Kasuwar Hatsi Ta Dawanau
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar bunkasa harkar noma ta jihar Kano (KSADP), za ta kashe kimanin Naira miliyan 600 domin gudanar da ayyukan inganta kasuwar hatsi ta kasa da kasa da ke Dawanau.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Malam Ameen Yassar, kwararre a fannin kula da ayyuka, wanda zai gudanar da ayyukan a Kano ya fitar
Ba mu da wata yarjejeniya da gwamnati na dakatar da shirin yajin aikin -Kungiyar Kwadago
Yassar ya ce, Bankin ci gaban Musulunci (IsDB) tare da hadin guiwar Asusun inganta jin dadin rayuwa (lives and livelihood funds) ne suka dauki nauyin shirin.
Ya ce, ayyukan da za a gudanar, sun hada da titi mai nisan kilomita hudu, magudanar ruwa da fitulun kan titi, inda ya ce, an bayar da wannan kwangilar ne ga kamfanin Labour Technical Services Ltd, kan kudi Naira miliyan 508.
Yassar ya kara da cewa, an baiwa kamfanin AITEC Infraconsult Ltd kwangilar gina gidan wanki guda uku da masallaci da ofishin ‘yansanda da ofisoshi da dakin taro, a kan kudi naira miliyan 92.
Ya ce, ana sa ran kammala aikin cikin watanni 12.