Connect with us

News

Ba mu da wata yarjejeniya da gwamnati na dakatar da shirin yajin aikin -Kungiyar Kwadago

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, ta ce babu wata yarjejeniya tsakaninta da gwamnatin tarayya na janye yajin aikin da ta shirya yi a ranar 3 ga watan Oktoba.

Advertisement

Kamar yanda Mista Benson Upah, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.

Rundunar sojin sun ce sun kashe ”yan ta’adda 191

Kungiyar Kwadago ta NLC Da TUC Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki Mai Dogon Zango Ranar Talata 3 Ga Oktoba 2023

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa a karshen taron majalisar zartaswar kungiyar kwadago ta kasa NLC da TUC sun shelanta yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata don janyo hankalin gwamnati ta amsa bukatunsu.

Advertisement

Upah yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da ake zargin Mista Olajide Oshundun, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka ya fitar.

Upah ya ce akwai wasu sabani a cikin sanarwar da suka hada da yajin aikin da ake shirin yi da kuma mamaye sakatariyar kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) ba bisa ka’ida ba.

“Saboda haka, mun ga ya zama dole mu yi karin haske. Na farko dai ba mu da wata yarjejeniya da gwamnati na dakatar da shirin yajin aikin.

Advertisement

“Ba mu da wata rana da za mu gana da gwamnati da za ta kai ga dakatar da yajin aikin da ake shirin yi.

“Duk da cewa ba mu da niyyar wulakanta ofishin mai girma Ministan Kwadago da Aiki, wannan lamari ya wuce ma’aikatar.

Ya kara da cewa “Ya kamata wannan ya fito fili a gare su yayin ganawarmu ta baya-bayan nan.”

Advertisement

Don haka ya yaba da rawar da Ministan Kwadago da samar da Aiki, Mista Simon Lalong ya taka wajen ganin an sako shugabannin NURTW daga tsaren ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *