News
Wasu Ƴan Bindiga Sun Yi Ɓarin Wuta A Funtua
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Funtua da ke karamar hukumar Funtua a jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutum daya a daren ranar Litinin.
Wanda lamarin ya rutsa da shi, kansila ne mai wakiltar mazabar Nasarawa ta karamar hukumar Funtua, Samaila Buhari Mairago, an ce an kai masa hari ne a gidansa da ke unguwar Nasarawa a cikin garin.
Ba a dai bayyana dalilin kashe shi ba, amma ana zargin samun rashin nasara ne wajen kokarin yin garkuwa da shi. Da yawan masu amfani da shafukan sada zumunta sun tabbatar da harin da kuma mutuwar kansilan.
Rahotanni na nuni da cewa, yankin na fama da hare-haren ‘yan bindiga akai-akai a ‘yan kwanakin nan.
Wani labarin kuma Wutar Lantarki Ta Yi Ajalin Mutum Hudu A Jahar Taraba
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro