News
Attajiri Ya Tausayawa Mutane a Kano, An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Attajirin Borno da ya karbi aron gidan mai saboda ya rangwantawa al’umma a Kano Alhaji Ibrahim Jibrin Mohammed ya saida litar man fetur da rangwamen N200 a unguwar Tal’udu Mai kudin ya yi irin wannan taimako a wasu garuruwan, kuma zai cigaba da karya farashin fetur
Attajirin dan jihar Borno wanda hannunsa a bude yake wajen kyauta, Ibrahim Jibrin Mohammed,
ya taimakawa mutane a Kano. Daily Trust ta ce a ranar Laraba, Alhaji Ibrahim Jibrin Mohammed ya karyawa mutane farashin man fetur, ya saida masu duk lita a kan N415. Man fetur da mutane su ka saya a kan N615 a gidan man kamfanin NNPCL da ke Tal’udu a Kano, ya koma N415 a sanadiyyar wannan attajiri.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
