News
Jamiyyar NNPP ta bayyana cewa wadanda suka gudanar da zanga-zanga a Landan ‘yan Najeriya ne masu kishin kasa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bayyana cewa wadanda suka gudanar da zanga-zanga a babban ofishin jakadancin Najeriya da ke Landan a ranar samun ‘yancin kai, ‘yan Najeriya ne masu kishin kasa da ke zaune a kasashen ketare, wadanda kawai suka nuna bacin ransu kan abin da suke gani a matsayin rashin adalci.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Wasu ‘yan Najeriya sun yi zanga-zanga a Landan kan hukuncin da kotun Sauraren Kararakin zabe ta Kano ta yanke wanda masu ruwa da tsaki na APC ta soki lamirin.
Majalisar Dattawa ta Tabbatar da Nadin Magajin El’Rufa’i a Matsayin Minista Dasu mutum 2
Sai dai a wata sanarwa da kakakin jamiyyar NNPP, Barista Ladipo Johnson ya fitar yace .
Jam’iyyar ta kuma bayyana wa manema labarai a Abuja ranar Talata, ta ce masu zanga-zangar ‘yan Najeriya ne masu kishin kasa kuma ta lura cewa matakin da suka dauka na nuna bacin ransu ne kan rashin adalcin da aka nuna a hukuncin da aka yanke kan al’amuran zaben gwamnan Kano.
Johnson ya bayyana cewa kamata ya yi jam’iyyar APC ta fara fahimtar cewa zanga-zangar, ko da mutum daya ne, yana da muhimmanci kuma ya kamata ta lura da irin wadannan matsaloli da sakonnin da suka dace a cikin zanga-zangar kamar ‘yancin fadin albarkacin baki, da zanga-zanga, su ne muhimman dimokuradiyya.
“Kamar yadda muka sani wadancan masu zanga-zangar ‘yan Najeriya ne mazauna kasashen waje wadanda kawai suka yi tir da abin da suke gani a matsayin rashin adalci kamar yadda suka shelanta a allunansu.”
Sanarwar ta kuma musanta duk wani ikirarin da ake yi na yakar gwamnati ko hukumomin gwamnati amma masu zanga-zangar sun ce kawai bangaren shari’a na bukatar taimako domin samun ‘yancin kai na gaske.
“Sai dai zanga-zangar da wadancan ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka yi ya jawo hankalin al’ummar duniya cewa a halin yanzu bangaren shari’a na Najeriya na bukatar taimako domin samun ‘yancin cin gashin kai da gaske, don haka sabanin irin wadannan munanan kalamai da jam’iyyar APC ta yi, masu zanga-zangar sun jaddada wannan batu ne kawai a maimakon haka. fada da bangaren shari’a ko kuma wata hukuma
ta gwamnati”.
