Entertainment
An ɗaure ƴar TikTok kan cin mutuncin shugaban ƙasa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata mai faɗa a ji a shafukan sada zumunta a Angola za ta sha daurin shekaru biyu a gidan yari saboda “cin mutuncin” shugaba João Lourenco a kan TikTok.
Kotu ta yankewa Ana da Silva Miguel, wanda aka fi sani da Neth Nahara, hukuncin ɗaurin watanni shida a watan Agusta.
Sai dai wata kotun daukaka kara ta yanke cewa hukuncin ya kasance mai sassauci inda ta kara shi zuwa shekaru biyu.
Ms Miguel ta zargi shugaban ƙasar a shafinta na TikTok da janyo “hargitsi da rashin tsari”, in ji kafofin watsa labarai na cikin gida.
Ta kuma jinginawa shugaban kasar laifin rashin makarantu da gidaje da kuma ayyukan yi a a kasar mai arzikin man fetur.
Kotun daukaka karar da ke Luanda babban birnin ƙasar, ta ce Ms Miguel ta yi amfani da kalaman batanci ga shugaban ƙasar, kuma kasancewar ta na da ikon yin tasiri a kan ra’ayin jama’a ya karawa lamarin muni
A wani labarin kuma Kudin Kilon Gas Din Girki Ya Kai N1,200
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.