Connect with us

News

Duk kasar da ba za ta iya samar da abinci ga al’ummarta ba, tana cikin tashin hankali – RIPAN

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Kungiyar masu sarrafa shinkafa ta kasa (RiPAN) ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci gwamnatin tarayya da ta sake duba matakin da ta dauka na janye dokar hana shigo da shinkafa daga kasashen waje kamar yadda ta sanar.

Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar reshen Kano kuma Shugaban Kamfanin Fursa Food LTD Alh. Abba Dantata ya yi wannan roko ne a jiya a Kano yayin wani taron manema labarai da kungiyar ‘yan jarida ta Kano Online ASKOJ.

Advertisement

Dalibin Jami’ar Gombe Ya Rasu Yana Tsaka Da Rubuta Jarrabawar Karshe

A cewarsa, duk da cewa gwamnatin tarayya ba ta fito ta bayyana wa jama’a da sauran masu ruwa da tsaki dalilin da ya sa aka dage haramcin a daidai lokacin da ake karfafa noman cikin gida ba, RPAN ta dauki matakin a matsayin ‘ba daidai ba’, wanda zai iya lalata masana’antun shinkafa na cikin gida.

Dantata ya ce, gwamnatin da ta gabata ta yi tanadi da yawa don karfafa noman shinkafa a kasar nan wanda wannan gwamnati mai ci gaba ce, bai kamata a yi tsammanin za ta mayar da ci gaban da aka samu a wannan fanni ba.

Advertisement

 

Ya ba da shawarar cewa, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta kara himma wajen inganta ababen more rayuwa da za su kara samar da shinkafa cikin sauki da arha ba tare da bude iyakokin kasar waje don shigo da ita ba wanda hakan zai tilasta wa da yawa daga cikin mambobinsu rufe ta yadda za a samu karin rashin aikin yi.

Advertisement

Sai dai Abba ya dora laifin karancin shinkafa, matsakaitan masu kudi da kuma rashin daidaiton farashin kudaden waje da dai sauransu, a matsayin wasu manyan abubuwan da ke haddasa tsadar shinkafar gida wanda dole ne gwamnati ta samar da hanyar da za ta bi wajen duba wadannan matsaloli tare da samun mafita mai dorewa.

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa bayan shekaru takwas, babban bankin Kasa, CBN, a ranar 12 ga watan Oktoba, 2023, ya bayyana janye takunkumin da ya sanyawa shigo da shinkafa da wasu kayayyaki 42 daga kasashen waje.

Advertisement

Sai dai dan kasuwar ya kara da cewa a kashin kansa, ya yi imanin gwamnati na da kyakkyawar niyya kuma ba za ta kawo cikas ga kokarin da ake yi na karfafa noma a kasar nan ba.

Ya kuma kara da cewa dole ne gwamnatin tarayya ta samar da tsare-tsare da za su kare harkar noman shinkafa na cikin gida idan har an bar shinkafar waje ta shigo cikin kasar nan domin kaucewa fita daga sana’ar.

Advertisement

Ya bukaci shugaba Tinubu da ya yi kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen shigo da shinkafa daga kasashen waje, yana mai cewa, “Idan gwamnati ta yanke shawarar bude kan iyakokinta domin shigo da shinkafa, miliyoyin ‘yan Najeriya za su rasa ayyukansu, kum Ya masana’antar za ta durkushe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending