News
Dalibin Jami’ar Gombe Ya Rasu Yana Tsaka Da Rubuta Jarrabawar Karshe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani dalibin Jami’ar Jihar Gombe da ke zangon karatu na karshe mai suna Abubakar Muhammad, ya rasu yayin da yake tsaka da rubuta jarrabawar kammala makarantar.
Dalibin dai na karatu ne a sashen koyon aikin Akanta na jami’ar.
Mutum 38 Sun Mutu, Yayin Da Wasu 40 Suka Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe
Wani abokin karatun marigayin ya bayyanawa jaridar Aminiya cewa marigayin ya zo dakin rubuta jarrabawa a ranar sai rashin lafiya ta kama shi inda nan take aka garzaya da shi zuwa cibiyar lafiya ta jami’ar dan duba lafiyarsa.
Mutum 38 Sun Mutu, Yayin Da Wasu 40 Suka Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe
Sai dai a cewar majiyar, jikin dalibin ya tsananta, amma kafin nan rai ya yi halinsa, inda aka wuce da shi dakin adana gawarwaki a asibiti.
“Ya rasu a cibiyar lafiya ta jami’ar sannan daga bisani mataimakin shugaban sashen tsaro na jami’ar ya jagoranci daukar gawar zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin kwararru na Jihar Gombe tare da wasu abokansa da kuma wasu jami’an jami’ar,” in ji dalibin.
Da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da rasuwar dalibin.
Sai dai ya ce dama dalibin ba shi da lafiya a ranar tun kafin shigarsa dakin
zana jarrabawar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
