Connect with us

News

Mutum 38 Sun Mutu, Yayin Da Wasu 40 Suka Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Akalla mutum 38 ne suka rigamu gidan gaskiya yayin da wasu kuma su sama da 40 suke kwance a asibiti biyo bayan wani mummunar hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Potiskum da ke jihar Yobe a ranar Laraba.

Rahotanni na nuni da cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Nangere zuwa Potiskum da ke jihar.

Rundunar Yan sanda A Kano Sun Musanta Zargin Daukar Masu Laifi Aiki

LEADERSHIP ta gano cewa wata motar tirela ce da ta kwaso shanu daga kauyen Buduwa da ke karamar hukumar Jakusko ce ta yi taho mu kara da wata babbar motar.

“Matukin tirelan yana tsula gudun wuce kima kuma ya rasa iya shawo kan motar nan take ya bugi wata babbar mota da ke kira da Canter Model, inda ya murkushe mutane sama da 20 da jikkata wasu sama da 40,” a cewar ganau.

Advertisement

Wata majiya ta ce, tirelar ta kuma murkushe wadanda suka fado daga cikin daya babbar motar da ya buga.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa ko tabbaci da hukumar kiyaye aukuwar hadura (FRSC) ko sauran hukumomin tsaro a jihar suka fitar dangane da wannan mummunar hatsarin.

A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda A Kano Sun Musanta Zargin Daukar Masu Laifi Aiki

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending