Connect with us

News

Mutane 8 ne suka mutu, 15 suka jikkata a hatsarin motan Jigawa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Mutane 8 ne aka ruwaito sun mutu yayin da wasu 15 suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya afku akan hanyar Malam Madori zuwa Birniwa a jihar Jigawa.

Hatsarin wanda ya afku a daren Lahadi, ya hada da motocin a uku, Golf 3, J5, da Hilux (Akori-kura) dauke da fasinjoji daga Kasuwar Jaji-Maji a jihar Yobe, kamar yadda wani ganau ya shaidawa jaridar  DAILY POST.

Matar Da Mijinta Ya Yi Kokarin Zubar Mata Da Ciki Ta Haifi ’Yan 4 a jahar Oyo

Ya yi ikirarin cewa hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane y sakamakon wuce gona da iri  da motscin sukayi

Shugaban kungiyar masu motocin haya ta kasa NARTO a karamar hukumar Birniwa Alhaji Baba ya tabbatar wa da manema labari  afkuwar lamarin.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa an kai wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Birniwa.

A cewarsa, mutane 15 ne suka jikkata kuma a halin yanzu suna samun kulawar likitoci, yayin da aka tabbatar da mutuwar fasinjoji shida.

Shugaban karamar hukumar Birniwa Umar Baffa na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar marigayin a makabartar kauyen Makari da ke unguwar Fagi a karamar hukumar Birniwa.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending