News
Dama ta samu ga masu sha’awar karatun Aikin Dan Sanda
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Advertisements
Advertisements
Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta gayyaci masu sha’awar shiga jami’arta da su nemi shiga makarantar ta na kwas na goma na yau da kullun.
A wata sanarwa a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na rundunar Olumuyiwa Adejobi, ya ce aikin rajistar ta yanar gizo zai fara ne daga ranar 24 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Satumba, kuma an bude shi ne ga ‘yan Najeriya maza da mata masu shekaru 17 zuwa 21.
Sauran abubuwan da ake bukata sun hada da mallakar lambar shaidar zama ta kasa (NIN), da mafi karancin kiredit shida a zaurukan da ba su wuce biyu ba a WAEC/NECO ko makamancinsa, tare da katin kiredit a Turanci da Lissafi.
Haka kuma ana bukatar maki da bai gaza 180 ba a jarabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ta shekarar 2023, inda aka zaba makarantar ‘yan sanda ta Najeriya a matsayin cibiyar da ta fi cancanta.
Advertisements
