News
Ya Kamata Alumma su maida hankali wajen karfafa guywar masu hidimtawa kungiyoyi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Anbukaci kungiyoyin Alumma dasu maida hankali wajen karfafa guywar masu hidimtawa kungiyoyin domin samun cigaba mai dorewa.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Shugaban kungiyar Inuwar Unguwar Kofar Mata da kewaye Alhaji Adamu Kofar Mata shine yayi Kiran yayin kaddamar sabon offishin kungiyar tare da karrama wasu daga cikin yayan kungiyar da suka sadaukar dakai wajen cigaban kungiyar t Wanda aka gudanar a harabar ofishin Kungiyar dake Kofar Mata.
Kamfanin NNPCL Ya Gargadi Masu Ɓoye Fetur Don Tsoron Ƙarin Farashin Man Da Samun Ƙarancinsa
Adamu Wanda ya bayyana rawar da kungiyoyar Inuwar Unguwar Kofar Mata ke takawa musamman a bangaran samarda da tsaro da hadinkai da zaman lafiya tsakanin Alummar yankin tare da yabawa kokarin yayan kungiyar dake bada gudunmawa ta kowanne bangara domin cigaban Unguwar da yankin baki daya.
Anasa bangaran Mai Unguwar Kofar Mata Mal. Muhammad Jibril Muhammad
Wanda ya yabawa kokarin kungiyar wajen hada kan Alummar Unguwar, ya bukaci hadin kan sauran mawadatan yankin wajen Kara tallafawa ayyukan kungiyar.
Daya daga cikin Yayan kungiyar da aka karrama Mal. Salisu Abdullahi (AUGUST) ya yabawa kungiyar Inuwar Unguwar Kofar Mata bisa karramawar tare Alkawarin jajircewa domin samun nasara.
Mai Unguwar Kofar Mata Mal. Muhammad Jibril da Chief Majestry Ibrahim Al-mustapha Kofar Mata da sauran shugabannin kungiyar sun jagoranci kaddamar da sabon offishin kungiyar dake Hauren Kofar Mata cikin Birnin Kano.
