Connect with us

News

Kamfanin NNPCL Ya Gargadi Masu Ɓoye Fetur Don Tsoron Ƙarin Farashin Man Da Samun Ƙarancinsa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Kamfanin man fetur na kada, NNPCL, ya gargadi jama’ar kasar da su kiyayi sayen mai suna adanawa, don tsoron fuskantar karanci da karin farashin man.

Leadership ta rawaito cewa, gargadin ya biyo bayan karuwar jerin motoci ne a gidajen mai a sassan kasar a ‘yan kwanakin nan.

NNPC Limited, ya ce yin gargadin ya zama wajibi, bisa la’akari da yadda aka fara ganin layukan ababen hawa a gidajen mai a birnin Ikko, cibiyar kasuwancin kasar, da birnin tarayya Abuja da dai sauran wasu garuruwa na Nijeriyar.

Shekaru 17: Rashin Kammala Hanyar Kano Zuwa Maiduguri Na Janyo Asarar Rayuka 

Wata sanarwa da kamfanin man ya fitar, ta ba wa ‘yan Nijeriya tabbaci, cewa an gano bakin zaren dangane da abin da ya haddasa layukan ababen hawa a gidajen man.

Advertisement

NNPCL, ya ce abin da ya janyo wannan matsala shi ne raguwar dakon man daga ma’ajiyarsa da ke Apapa a birnin Ikko, wato Legas.

Amma yanzu haka akwai isasshen mai a adane, wanda aka yi amanna za a kwashe tsawon kwana talatin ana amfani da shi a kasar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Saboda haka, kamfanin man na Nijeriya ya yi gargadin cewa, jama’a su guji sayen man suna adanawa, bisa tsoron za a yi fama da karancinsa.

NNPCL, ya ce, nan da ‘yan kwanaki kadan komai zai daidaita game da safararsa zuwa sassan Nijeriyar.

Ana fatan wannan sanarwa da kamfanin man ya bayar, za ta kwantar wa jama’ar kasar hankali, ta kuma kawar da duk wata fargabar da ake yi, cewa mai yiwuwa an hau hanyar fama da karancin man, ko kuma an fara take-taken da za a kara farashinsa.

A wani labarin kuma Shekaru 17: Rashin Kammala Hanyar Kano Zuwa Maiduguri Na Janyo Asarar Rayuka 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending