Connect with us

News

ASUU Ta Bai Wa ‘Yan Gudun Hijira 320 Tallafin Kayan Abinci A Jahar Katsina

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta raba kayan abinci ga ‘yan gudun hijira 320 da ke jihar Katsina a ranar Lahadi.

Advertisement

Dakta Lawalli Alkali, shi ne ya wakilci shugaban ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Victor Emmanuel a yayin rabon kayan rage raɗaɗin.

Shugaba Tinubu Ya Ce Har Yanzu Najeriya Rarrafe Take Ta Fuskar Ci Gaba

Ya ce, wannan ba shi ne irinsa na farko da ƙungiyar ta ke yin irin wannan tallafin ba, inda ya ce, irin wannan na ɗaukan lokaci kafin su yi, amma ba shi ne na farko ba.

Advertisement

Ya ce, kayan abincin sun haɗa da shinkafa, mangyaɗa, taliyar leda, taliyar yara, magin ɗanɗano da dai sauransu.

Ƙungiyar ta ce, ta fahimci ‘yan gudun hijira a matsayin mutanen da ke fama da matsala da ke tsananin buƙatar tallafi da agaji, don haka ne ƙungiyar ta ayyanasu cikin al’ummar da ke neman tallafi.

Advertisement

Alkali ya roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi dukkanin mai yiyuwa domin shawo kan matsalolin tsaro da suke faɗin ƙasar nan domin bai wa ‘yan gudun hijira damar komawa gidajensu na asali.

A cewarsa, ASUU na bibiyar lamura a jihar Katsina don haka ne suka jinjina wa ƙoƙarin gwamna Dikko Radda na matakan da ya ke ɗauka kan matsalar tsaro.

Advertisement

Leadership ta rawaito cewa Wasu ‘yan gudun hijiran waɗanda mafi yawansu mata ne sun yaba wa ƙungiyar ASUU bisa tallafin, inda suka roƙi gwamnatin jihar da ɗaiɗaikun mutane su ma da su taimaka musu.

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu Ya Ce Har Yanzu Najeriya Rarrafe Take Ta Fuskar Ci Gaba

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending