Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Ce Har Yanzu Najeriya Rarrafe Take Ta Fuskar Ci Gaba

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa har yanzu Najeriya rarrafe take ta fuskar ci gaba, amma gwamnatinsa ta dauki aniyyar sauya wa lamarin akala ta hanyar jagoranci na gari.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a wannan Lahadin, yayin zantawa da Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz da tawagarsa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

An tsinci wani mutum da ransa bayan sati biyu da ɓacewarsa a Teku

Shugaban ya kuma yi kiran da a inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Jamus musamman a fannin tsaro, albarkatun kasa, ilimi, demokradiyya da sauransu.

Advertisement

Shugaba Tinubu, wanda ya ce hukuncin tabbatar da zabensa da Kotun Koli ta yi a makon jiya, ya sanya a yanzu ya mayar da hankalinsa ne kacokam kan ciyar da kasar gaba.

Ya ce yana maraba da inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da gwamnatin Jamus ta fannoni da dama.

Advertisement

“Har yanzu Najeriya rarrafe take yi, amma mun kuduri aniyar ganin an sauya salo da samar da gwamnatin da za ta kawo sauyi a kasar,” in ji shugaba Tinubu.

A nasa jawabin, Shugaban Gwamnatin Jamus Scholz, ta jaddada bukatar kara inganta hadin gwiwa kan ababen more rayuwa, musamman a bangaren wutar lantarki da makamashi.

Advertisement

Kazalika, ya yi wa shugaba Tinubu godiya kan rawar da ya taka a kungiyar ta Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS), inda ya yi kira da a hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka da ma duniya baki daya.

Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayo iskar gas daga Najeriya da nufin cike gibin makamashi da kasarsa ke fama shi tun bayan raba gari da Rasha sakamakon mamaye Ukraine da ta yi.

Advertisement

A gabanin fara wata ziyarar aiki a Abuja da Legas da Accra, Scholz ya bayyana wa kafar yada labaran Daily Punch cewar kamfanonin gas na kasar Jamus na duba yiwuwar kulla alakar kasuwanci da Najeriya.

Scholz wanda ya yaba dimbin arzikin makamashin gas da Najeriya ke da shi, yana duba yiwuwar hada gwiwa da fadar mulki ta Abuja wajen bullo da wata sabuwar hanya samun sinadarin hydrogen.

Advertisement

Jagoran na Jamus na son kulla alaka mai karfi da tarayyar Najeriya a wani abin da ya kira bani gishiri in baka manda a tsakaninsu.

Wannan shi ne karo na 3 da shugaban gwamnatin Jamus ke kai ziyara a kasashen Afirka a kokarin fadada alakar kasarsa tun bayan darewa madafun iko kasa da shekaru biyun da suka gabata.

Advertisement

Bayan ganawa da mahukuntan na Najeriya shugaban gwamnatin Jamus Sholz zai je Lagos kafin ya karasa Ghana inda a can ma zai tattauna batuwan cinikayya a tsakanin kasashen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending