Connect with us

News

Kamfanin NNPC ya ba da tabbacin cewa zuwa karshen shekarar 2024 za a kammala aikin bututun iskar gas na Ajaokuta-Kano 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kamfanin NNPC ya ba da tabbacin cewa zuwa karshen shekarar 2024 za a kammala aikin bututun iskar gas da ya tashi daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK).

 

Advertisement

Shugaban Rukuncin Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce bututun iskar gas din wanda aka kammala kashi 80 cikin 100 zai kara sada yankin Arewa da Neja Delta da ma sauran sassan Najeriya.

An Sace Dagaci Da Sauran Mutane A Wani Harin ‘Yan Bindiga A Jahar Zamfara

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Mele Kyari ya bayyana haka ne ta bakin mataimakinsa mai kula da bangaren Iskar Gas da Makamashin Zamani, Olalekan Ogunleye, a yayin rangadin bangaren aikin da aka kammala a yankin Kogin Hadejia.

Advertisement

Olalekan ya ce, “za mu ci gaba da bayar da muhimmanci ga kammala aiki a kan lokaci, don haka tilas mu kara hada karfi da karfe wajen tabbatar da an kammala wannan aiki mai muhimmanci ga habaka tattalin arzikin Najeriya.”

Ya kuma yaba wa kamfanin BRENTEXCCP Limited da aka ba wa aikin shimfida bututun iskar gas din, ganin cewa kawo yanzu ba a samu rauni ko asarar rai ba a tsawon awa miliyan 7.2 da daukacin ma’aikata suka shafe a kansa.

Advertisement

Mataimakin shugabna kamfanin na BRENTEXCCP Limited, Sani Abubakar, ya ba da tabbacin cewa za a kammala shimfida bututun iskar gas din kafin cikar wa’adin da gwamnati ta ba su, domin duk abubuwan da ake bukata na aikin suna kasa.

A wani labarin kuma An Sace Dagaci Da Sauran Mutane A Wani Harin ‘Yan Bindiga A Jahar Zamfara

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending