Connect with us

News

An Sace Dagaci Da Sauran Mutane A Wani Harin ‘Yan Bindiga A Jahar Zamfara

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wasu ‘yan bindiga sun shiga wani kauye a jahar Zamfara inda suka sace wani dagaci da sauran Mutane

Yan bindiga sun mamaye garin Yashi da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara inda suka kashe daya, suka yi awon gaba da basaraken gargajiya a yankin, da wasu mutane 4.

Advertisement

Rundunar ‘Yan sanda Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Sace A Jihar Katsina

Yan bindigar sun kuma hana mutanen yankin shiga gonakinsu, don haka ba za su iya girbe amfanin gona ba.

Me wakiltar mazabar Bukkuyum ta kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kan al’ummar a daren Juma’a da misalin karfe 3 na rana, inda suka kwashe wani dan unguwar tare da wasu mutane 5 ciki har da sarkin gargajiya.

Advertisement

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun zage damtse wajen ganin an dakile ‘yan fashin daga kwashe wadanda aka sace su nesa da al’umma.

Ya ce nan ba da dadewa ba za a ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma yi kira da a kwantar da hankula a cikin al’umma, ya kuma kara da cewa Gwamnan ya damu matuka da yanayin tsaro a jihar, kuma bai ja da baya ba wajen ganin an shawo kan matsalar.

Advertisement

A wani labarin kuma Rundunar ‘Yan sanda Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Sace A Jihar Katsina

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending