News
Rundunar ‘Yan sanda Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Sace A Jihar Katsina
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ceto wasu mutum hudu da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da su a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Aliyu ya ce, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar Katsina, rundunar ‘Yansanda tare da hadin guiwar sojojin Nijeriya sun ceto mutane hudun da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a fadid jihar.
Kakakin ‘Yansandan ya jaddada cewa, sun gudanar da aikin kubutar da mutanen ne yayin aikin sintiri da suke gudanarwa kullum a kauyen Dankolo, karamar hukumar Dandume da ke jihar.
“A yau, 28 ga Oktoba, 2023, da misalin karfe 08:30 na safe, rundunar hadin guiwar ‘Yansanda da jami’an soji sun yi nasarar kubutar da mutum hudu wadanda aka yi garkuwa da su.” Cewar Kakakin ‘Yansanda.
Rundunar ‘Yansandan jihar ta bukaci al’ummar jihar da su bayar da hadin kai wajen kai rahoton duk wani abu da suka samu ko wani mutum zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
A wani labarin kuma Kamfanin da ke rarraba wutar lantarki na KEDCO ya ce za a samu daukewar wutar lantarkin na tsawon awanni 12
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
