Connect with us

News

Ana zargin wani matashi da kisan karamin yaro tare ƙwaƙwule masa Idanu a Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ana zargin wani matashi da kisan karamin yaro tare ƙwaƙwule masa Idanu a Kano

Nassara Radio ta rawaito cewa Lamarin ya faru ne da  safiyar ranar Lahadi Unguwar Dandago dake birnin Kano.

An  zargi matashi mai suna Dan Umma da hallaka wani yaro dan shekara biyar mai suna Muhammad Suyudi, ta hanyar yi masa yankan rago tare da ƙwaƙwule masa idonu.

Jami’an yan sanda sun tafi da matashin wanda ake zargin mutanen Unguwa sun dauki doka a hannunsu, ta hanyar sassara shi bayan sun same shi da gawar yaron, wanda shima yanzu haka yana kwance a Asibiti, kamar yadda mai Unguwar Dandago, Malam Muhammad Sani ya tabbatar.

Sai dai kuma dan uwan matashin mai suna Shazali, yace ƙanin nasa yana fama da lalurar kwakwalwa, ya kwanta a Asibitin Dawanau a ƙalla sau bakwai, yanzu ma bai dade da fitowa ba, kasancewar lalurar tasa motsi-motsi ce, a haka ba lallai a gane cewa bashi da lafiya ba sai idan ta motsa, amma dukda haka, Shazali yace a madadin danginsu, suna bada hakuri.

Advertisement

A wani labarin kuma Ana Harbe-Harbe A  Jahar Ribas Bayan Majalisar Jihar Ta Fara Shirin Tsige Gwama

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending