Politics
Burin Samar Da Ingantacciyar Najeriya Bai ‘Kare Ba – Peter Obi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dan takarar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya ce burinsa na ganin sabuwar Najeriya bai kare ba, duk da kotun koli ta yanke hukunci a ranar 26 ga watan Oktoba da ya gabata.
Obi ya yi magana ne a wani taron manema labarai a Abuja kimanin makonni biyu bayan kotun kolin ta tabbatar da nasarar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Cikin Shekara Biyar An Sace Danyen Mai Na Trilliyan 4. – NEITI
Obi, wanda ya caccaki hukuncin da kotun kolin ta yanke, ya amince da cewa an kawo karshen shari’ar zaben da ya gabata.
Ya ce har yanzuyana nan akan barkarsakuma gwiwarsaba zata yi sanyi ba.
Ko da yake bai fito fili ya bayyana ko zai sake tsayawa takarar Shugaban kasa a 2027 ba, ya ce ba a kawo karshen tafiyarsa ta neman samar da sabuwar Najeriya ba.
A wani labarin kuma Cikin Shekara Biyar An Sace Danyen Mai Na Trilliyan 4. – NEITI
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
