News
Fadar Shugaban Kasa Ta Mayar Da Martani Ga Peter Obi Kan Hukuncin Kotun Koli
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI
Gwamnatin Najeriya ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023 da ya wuce, ya rungumi salon yakin neman zabe na amfani da batutuwan kawo ci gaba, maimakon amfani da addini da kabilanci kamar yadda ya yi a zaben da ya wuce.
Gwanan Oyo ya yi wa ma’aikata ƙarin naira 25,000 a kan albashinsu
Ta ce ta rasa yadda Peter Obi wanda ta kira mai kwaikwayon abin da ya ga wani ya yi, da jam’iyyarsa ta LP suka hakikancewa kansu cewa su ne suka ci zaben da za a zahiri ya zo na uku.
Gwamnatin na mayar da martani ne ga wani taron manema labarai da Peter Obi ya gudanar ranar Litinin inda ta zarge shi da zubar da mutuncin bangaren shari’a.
Ta ce dan takarar na jam’iyyar LP a zaben da ya wuce, yayin taron manema labaran da ya gudanar, tamkar Atiku Abubakar, ya yi kokarin zubar da mutuncin Kotun Koli da hukumar zabe ta INEC saboda a cewar gwamnati, don kawai ba su ayyana shi matsayin wanda ya ci zaben 25 ga watan Fabrairu ba.
Ta ce kamaya ya yi a zurfafa nazari kan babban mafarkin Peter Obi, wanda ya yi imanin cewa zai iya cin zabe ta hanyar gudanar da yakin neman zabe mafi haddasa gaba da janyo rarrabuwar kawuna da ya gwara kan Kiristoci da Musulmai da kuma wannan kabila da wata a kasa mai yawan kabilu da yawan addinai kamar Najeriya.
Sanarwar da Babban Mashawarcin Tinubu kan harkar yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Peter Obi ya yi kokari ba tare da nasara ba wajen tunzura ‘yan Najeriya da karairayi da gugar zana, sannan ta zarge shi da yin tufaka da warwara.
Gwamnatin Tinubu ta ce Obi ya amfana da hukunce-hukuncen kotuna a baya amma a yanzu yana bata suna kotun saboda hukuncinta bai yi masa dadi ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
