News
Shugaban Majalisar Filato Da Mataimakinsa Sun Yi Murabus
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato, Moses Thomas Sule, ya yi murabus daga mukaminsa.
Kazalika mataimakinsa, Gwottaon Fom, shi ma ya ajiye mukaminsa.
Rashin sana’a ga matasa ne matsalar Nijeriya -Muhammad Zahraddin
Bayan haka ne aka zabi dan majalisa mai wakiltar Pankshin ta Arewa Gabriel Dawang, a matsayin sabon shugaban majalisar.
Honorabul Timothy Dantong mai wakiltar mazabar Riyom kuma a yanzu shi ne sabon mataimakin shugaban majalisar.
Aminiya ta ruwaito cewa hakan na da nasaba da kwace kujerar gwamnan jihar, Caleb Mutfwang da wasu ’yan majalisar dokokin jam’iyyar PDP da kotu ta yi.
A wani labarin kuma Rashin sana’a ga matasa ne matsalar Nijeriya -Muhammad Zahraddin
BBC ta fara jiyowa daga manyan jami’an gwamnatin Isra’ila game da yarjejeniyar sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Sun ce idan aka kammala ƙulla ta, za a saki Isra’ilawa 50 “cikin kwana huɗu” – 12 ke nan a kowace rana.
Wani babban jami’in gwamnatin ya ce dukkan hukumomin tsaro, na soja da masu tattara bayanan sirri na Isra’ila, sun amince da ƙunshin yarjejeniyar – bayan sun ƙi amincewa da wata wadda Qatar ta jagoranta tun farko.
Jami’in ya kuma ce: “Bugu da ƙari, ƙila Hamas ta saki wasu bisa raɗin kanta. Kawai dai, yarjejeniyar za ta ƙunshi sakin kamar mutum 80.”
-
News6 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News7 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News4 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
