Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya ta Soke Lasisin Kamfanonin Hakar Ma’adanai Sama Da Guda 1000

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu
Advertisements
ads

FAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Gwamnatin tarayya ta kwace Lasisin hako Ma’adanai guda 1,633 da aka baiwa kamfanonin hakar ma’adanai da ba su bi ka’ida ba.

Ministan ma’adanai da cigaba, Dele Alake ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata.

Shugaban Majalisar Filato Da Mataimakinsa Sun Yi Murabus

Ya ce an soke lasisin wadannan masu mallakar ma’adanan ne saboda rashin biyan kudaden hidima na tilas na shekara na Naira 1,500 ga kowane bangare na cadastral.

Ya ce, “Ofishin Cadastre na Ma’adinai ya ba da shawarar soke sunayen ma’adanai guda 1,633 kamar haka: Lasisi na Bincike guda 536; Lasisi na Quarry guda 279; Lasisin Kananan Ma’adinai guda 787 da Hayar Ma’adinai guda 31.

Advertisement

“Dangane da ikon da NMMA shekarar 2007, Sashe na 5 (a) ta ba ni, na amince da soke sunayen ma’adanai wadanda aka ambata guda 1,633.”

A wani labarin kuma Shugaban Majalisar Filato Da Mataimakinsa Sun Yi MurabusFiraministan Isra’ila ya ce ana samun “cigaba” a yunƙurin ƙulla yarjejeniyar da za ta kai ga sakin mutanen da mayaƙan Hamas ke garkuwa da su a Zirin Gaza.

Benjamin Netanyahu ya ce: “Ina fatan za a samu labari mai daɗi.”

Kafofin yaɗa labaran Amurka, da na Qatar, da sauran kamfanonin dillancin labarai sun ruwaito cewa ana dab da ƙulla yarjejeniyar, wadda ƙasar Qatar ke jagoranta tsakanin Hamas da Isra’ila.

A jiya Litinin ma Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya yi “imanin hakan” bayan wani ɗan jarida ya tambaye shi game da yarjejeniyar da aka ce an kusa ƙullawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending