Connect with us

News

Wata Gobara  ta tayi Mummunar barna a hukumar Shari’a ta jihar kano

Published

on

Advertisements
ads

 

Gabora ta tashi a wani bangare na hukumar shari’a ta jihar kano a yau Talata, lamarin da ya janyo asarar dukiya mai tarin yawa a ofisoshin dake bangaren.

Jaridar Indaranka ta rawaito Hajiya Batulu Isah Waziri babbar daractan kudi da mulki ta tabbatar da faruwar lamarin, Inda ta ce wutar ta faraci misalin karfe 01:30 dai dai lokacin da aka shiga sallar azuhur.

Gwamnatin Tarayya ta Soke Lasisin Kamfanonin Hakar Ma’adanai Sama Da Guda 1000

Ta ce wutar ta kone ofisoshin da ke ɓangaren, amma ba a samu asarar rai ba, sai dai ta dukiya.

Jami’an kashe gobara sun sami nasar kashe gobarar bayan da jami’an mu suka sanar da su faruwar lamarin. In Ji Batulu

Hukumar shariah dai itace hukumar da ke kula da abin da ya shafi harkokin addini, masallatai

Advertisement

da makarantun addini da abinda ya shafi lokutan sallah da Nisabin zakka da sauransu.

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya ta Soke Lasisin Kamfanonin Hakar Ma’adanai Sama Da Guda 1000

An samu takaddama a majalisar dattijan Najeriya ranar Talata, bayan sanar da nadin shugabanni a bangaren marasa rinjaye da Shugaba Majalisar Godswill Akpabio ya yi.

Kujerar shugaban marasa rinjaye da ta mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye sun kasance babu kowa tun bayan da kotun daukaka kara ta soke zaben Sanata Simon Davou Mwadkwon na PDP da Darlington Nwokocha na LP.

Kotu ta soke zaben sanata Simon Mwadkwon inda ta ba da umarnin sake gudanar da zabe.

Tun a makon jiya ne sanatocin jam’iyyar PDP suka gudanar da wani taron gaggawa kan batun maye guraben shugabannin marasa rinjaye.

Advertisement

Jaridar Punch ta ambato Sanata Garba Maidoki wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron, na cewa ‘yan majalisa bangaren adawa sun amince sun amince da fitar da sabon shugaban marasa rinjaye daga arewa ta tsakiya.

Don haka, yayin zaman majalisar na Talata, Godswill Akpabio ya sanar da Abba Moro na PDP a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Osita Ngwu shi ma daga PDP zai kasance mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye.

Shugaban majalisar ya ce sabbin shugabannin marasa rinjayen sun samu rinjayen goyon bayan takwarorinsu.

Da yake gabatar da wnai kudurin jan hankali, Sanata Okechukwu Ezea na jam’iyyar LP ya nuna rashin amincewa da rashin shigar da jam’iyyarsa a shugabancin marasa rinjaye, inda ya bayyana lamarin a matsayin rashin adalci ga jam’iyyun marasa rinjaye.

Ana cikin hargitsi ne, sai Sanata Tony Nwoyi na LP ya zargi Godswill Akpabio da nada wa jam’iyyun adawa shugabanci.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending