Connect with us

News

Bayan Kwana 50 Masu garkuwa Sun sako dalibar jami’a

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

Yan sanda sun ceto daya daga cikin dalibai mata biyar da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina.

Advertisement

An yi nasarar ceto dalibar ce bayan wani samame da Rundunar ’yan sandan ta kai a ranar Litinin.

Majalisa Wakilai Ta Amince Wa Gwamnatin Tarayya Kashe Naira Tiriliyan 26 Daga 2024 Zuwa 2026

A cewar kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu, an ceto dalibar wadda ba a bayyana sunan ta ba saboda dalilai na tsaro ne a kauyen Bilbis da ke Jihar Zamfara makwabciyar Jihar Katsina.

Advertisement

Ya jaddada kudirin rundunar na yin amfani da wadatattun kayan aiki don ceto sauran daliban hudu daga da aka yi garkuwa da su.

“Yayin da wadda aka ceto ke samun kulawar likita, Kwamishinan ’Yan sanda ya jinjina wa jami’an rundunar, ya kuma bukaci jama’a su rika taimakawa da bayanai masu muhimmanci don inganta tsaro,” in ji sanarwar.

Advertisement

A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023, mahara suka sace dalibai mata biyar a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, inda daga bisani ’yan sanda suka tabbatar da kama daya daga cikin wadanda ake zargi da sace daliban.

An sace daliban ne a gidansu da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri Memorial International daura da hanyar Tsaskiya.

Advertisement

A wani labarin kuma Majalisa Wakilai Ta Amince Wa Gwamnatin Tarayya Kashe Naira Tiriliyan 26 Daga 2024 Zuwa 2026

Rahotanni daga birnin Tarayyar Najeriya, Abuja na cewa an yi garkuwa da wasu mata takwas a yankin Kuje.

Advertisement

Wannan labari na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 da sace mataimakin shugaban karamar hukumar Kwali da wasu mutane shida a kauyen Yewuti da ke Kwalin.

Matan da manoma ne an sace su ne a wata gona da ke kauyen Gwombe da ke masarautar Gwargwada a karamar hukumar Kuje.

Advertisement

Wani mazaunin Gwargwada, Usman Yakubu ya shidawa jaridar Daily Trust ta Najeriya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.

Ya kuma kara da cewa wasu ‘yan bindiga ɗauke da bindigogi kirar AK-47 ne suka yi awon gaba da matan, wadanda dukkaninsu matan aure ne da ke aikin girbi a gonakinsu.

Advertisement

Wani basaraken kauyen da ya zaɓi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace mutanen, sannan ya zargi cewa maharan ‘yan bindiga ne daga Kebbi da ‘yan banga Miyetti Allah suka tarwatsa a karshen mako.

Babu wani martani daga kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, kan lamarin kawo yanzu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending