Connect with us

News

Majalisa Wakilai Ta Amince Wa Gwamnatin Tarayya Kashe Naira Tiriliyan 26 Daga 2024 Zuwa 2026

Published

on

DAGA AISHA BASHIR MUSA

 

Advertisement

Majalisar wakilai ta amince da kudirin gwamnatin tarayya na kashe naira tiriliyan 26 a tsakanin 2024 zuwa 2026.

Daga cikin wannan adadin da aka amince da shi, Naira tiriliyan 10.2 na yau da gobe ne daga cikin kudin da gwamnatin ke samu (ba bashi); Ma’aikatu (MDAs) za su lakume Naira Tiriliyan 4.49; bukata ta musamman da ka iya bijirowa, an ware mata Naira biliyan 200; an kuma tanadi Naira Tiriliyan 5.9 domin manyan ayyuka tare da wata bukata ta musamman akan Naira biliyan 7.

Advertisement

Kotu Ta Bayar Da Belin Emiefiele Akan Naira Miliyan 300

Majalisar ta kuma amince da bukatar samar da karajin haraji na Naira tiriliyan 16.9; Cike gibin da aka samu a Kasafin kudi na Naira Tiriliyan 9, ta kuma amince a amso Naira Tiriliyan 7.8 a sabon rance (ciki har da karbar rance daga kasashen waje da cikin gida).

Wannan amincewar ta biyo bayan la’akari da karbar shawarwarin da rahoton Tsarin Kudi na Matsakaici na 2024-2026 (MTEF) da Takarda Dabarun tsimi da tanadi (FSP) na zauren majalisar ya bayar a ranar Talata.

Advertisement

Hon James Faleke (APC, Legas) ne ya gabatar da rahoton ga kwamitocin kudi, tsare-tsare na kasa da bunkasa tattalin arziki da bada tallafi, lamuni da kula da basussuka kuma kwamitin samar da kayayyaki wanda kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya yi duba acikin rahoton a matsayin shugaba kuma ya amince da shi a zaman majalisar.

A wani labarin kuma Kotu Ta Bayar Da Belin Emiefiele Akan Naira Miliyan 300

Advertisement

An kai hari hedikwatar ‘yan sanda da ke Adamawa a sanyin safiyar Laraba, lamarin da ya ɗaga hankula da jefa al’umma cikin yanayi na kaɗuwa a birnin Yola.

An shafe kusan rabin sa’a ana harbe-harbe, a cewar mazauna kusa da hedikwatar.

Advertisement

Wasu majiyoyi na cewa sojoji ne suka kai harin na ramuwa, bayan sun zargi wani ɗan sanda da kashe wani jami’insu.

Wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sanda CP Afolabi Babatola, ya fitar ta tabbatar da harin tare da Allah-wadai da rikicin da ya ɓarke tsakanin jami’an ‘yan sanda da sojoji.

Advertisement

A cewar sanarwar rikici ne ya rikiɗe zuwa musayar harbe-harben bindiga wanda ya kai ga wani mummunan hari kan ofishin ‘yan sanda da ya yi sanadin mutuwar wani Sufeto, Jacob Daniel.

CP Babatola ya bayar da umarnin a gudanar da bincike cikin gaggawa domin tabbatar da adalci da kuma dawo da zaman lafiya.

Advertisement

Ya kuma jaddada cewa ba za a sake lamuntar duk wani hari da ake kai wa jami’an tsaro a bakin aiki.

Babatola ya jaddada muhimmanci rayuwar dukkanin jami’an tsaro tare da shan alwashin cewa za a magance irin waɗannan rikice-rikicen bisa dokokin da ake dasu.

Advertisement

Kwamishinan ya kuma bayyana kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin kira da a haɗa kai a tsakanin rundunonin tsaro domin kare haƙƙinsu.

CP Babatola ya kuma buƙaci jama’a su kwantar da hankulansu, inda ya tabbatar cewa manyan jami’an tsaron biyu na aiki tukuru bisa tsarin doka don shawo kan duk wata matsala ta tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending