News
Kotu Ta Bayar Da Belin Emiefiele Akan Naira Miliyan 300
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maitama, ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
An bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 300 wanda kuma dole wadanda zasu biya kudaden su kasance ‘yan Nijeriya kuma ma’aikatan gwamnati masi gida ko filaye a babban birnin tarayya Abuja.
Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin-gadi
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, Mai shari’a Hamza Muazu ya ce Emefiele ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda tabbas sun mallaki dukiya a gundumar Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja.
Emefiele bai kasance a gaban kotu ba yayin zaman na yau, inda aka tsare shi a gidan yarin Kuje a makon jiya.
Wata babbar kotun birnin tarayya ta bayar da umarnin a sake shi makonni biyu da suka gabata a cikin wata babbar kotu ta kare hakkin dan Adam da ya shigar a kan gwamnatin tarayya.
Kotun ta dage zaman har zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba domin fara shari’ar domin cigaba da sauraren kararrakin akan Emiefiele
A wani labarin kuma Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin-gadi
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
